31 Janairu 2026 - 11:07
Source: ABNA24
Mutum Daya Yayi Shahada A Harin Bam Da Gwamnatin Saudiyya Ta Kai Kan Iyakokin Yemen

An kashe wani farar hula sannan wani ya ji rauni a ranar Juma'a a wani harin da Saudiyya ta kai kan iyakokin lardin Saada, arewacin Yemen.

Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBayt: An kashe wani farar hula sannan wani ya ji rauni a ranar Juma'a a wani harin da Saudiyya ta kai kan iyakokin lardin Saada, arewacin Yemen.

Majiyoyin yankin sun ce bayana harba makaman roka da Saudiyya ta yi sun kai hari kan yankunan gundumar Shada a wani sabon ta’addanci da sojojin Saudiyya suke aikatawa na kai hari kan yankunan da ke kan iyakar.

Sojojin Saudiyya suna ci gaba da keta haddin da kuma kai hari kan fararen hula a yankunan da ke kan iyakar Yemen a lardin Saada na arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da kuma asarar dukiya.

Wannan laifin ta’addanci ya zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan jerin laifukan da rundunar sojin Saudiyya ta aikata, inda wani rahoto da jami'an tsaron Saada suka fitar ya bayyana cewa masu tsaron kan iyakar Saudiyya sun kai hari kan fararen hula a gundumar Qataber, Shada da Monabeh a ranar Alhamis da ta gabata, ta hanyar amfani da bindigogi da harsasai na manyan bindigogi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan Afirka, tare da jikkata wasu 'yan kasar da dama.

Your Comment

You are replying to: .
captcha